e-Naira: Babban Bankin Najeriya ya Sanar da Kamfanin Fasahar da Zai Aiki da Shi

 

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya sanar da sunan kamfanin fasahar da zai yi aiki da shi, Bitt Inc., a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira.

CBN ya zabi Bitt Inc. daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

A cewar Bankin, ya fi gamsuwa da kamfanin Bitt Inc. saboda wasu tsare-tsare da gwaje-gwaje da ya aiwatar kan kudin intanet, wanda dama tuni kudin da kamfanin ya samar an soma kashe su a kasashen gabashin Caribbean.

Sanarwar da CBN ya fitar ta kuma shaida cewa CBN ta lissafa wasu daga cikin alfannu kudin intanet din da suka hada da inganta tsarin kasuwanci tsakanin iyakoki, wadatuwar kudade cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here