Cutar Kwalara ta yi Sanadiyyar Kashe Mutane 83, Sama da 2,336 Sun Kamu a Nijar

 

Mahukunta a Nijar sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon barkewar kwalara a wasu sassan kasar, inda mutum sama da dubu biyu suka kamu.

Cuar a yanzu ta yadu tsakanin yankunan shida na kasar kuma ambaliyar da ake samu na sake yawaita masu kamuwa da cutar.

Tun daga soma samun barkerwa cutar a watan Maris zuwa yanzu mutum 83 sun mutu, sannan 2,336 sun kamu.

A cewar mahukunta ana daukan matakai domin dakile yaduwarta sai dai akwai bukatar mutane su ke kasancewa masu kula.

Ko a shekara ta 2018 sai da aka samu irin wannan mumunan barkewar kwalara a yankunan Zinder da Maradi da Dosso, akalla mutum 68 suka mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here