Cutar Sarkewar Numfashi: Amurka ta Ginawa Najeriya Katafaren Asibiti Don Kebe Masu Cutar

Kasar Amurka ta tallafawa Najeriya da ginin wani katafaren asibitin kebe masu Korona.

Kasar ta bayyana ci gaba da hadin kanta da Najeriya wajen yaki da Korona.

Hukumar lafiya ta Najeriya tare da jakadiyar Amurka a Najeriya sun bude asibitin a Abuja

Kasar Amurka ta bayar da gudummawar wani katafaren asibitin da zai taimakawa Najeriya wajen killace masu COVID-19, HumAngle ta ruwaito.

An bayar da gudummawar wurin ga Ma’aikatar Lafiya daga Ofishin Tsaro na Amurka reshen Afrika, tare da tallafin USAID, Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) da Walter Reed Army Institute of Research (WRAIR).

Mary Beth Leonard, Jakadiyar Amurka a Najeriya, tare da Olorunnimbe Mamora, karamin Ministan Lafiya, sun bude asibitin a ranar 22 ga Janairu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja, in ji Ofishin Jakadancin na Amurka a ranar Litinin.

An bayyana cewa asibitin zai iya daukar mutane 40 da za a kebe.

Leonard ta bayyana gudummawar dala miliyan 1.3 na asibiti a matsayin alamar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka.

Leonard ta kuma bayyana cewa gwamnatin Amurka na nan kan bakanta na tsayawa tare da Najeriya don tabbatar da cewa ana ci gaba da bunkasa kwarewa domin ba kasar damar inganta ci gaba da kulawa da kebe masu COVID-19.

Ta kara da cewa “Tallafawa ma’aikatan kiwon lafiya wadanda ke kula da marassa lafiya a wannan cibiya da kuma duk fadin kasar, yana da matukar muhimmanci ga kokarin Najeriya na rage yaduwar COVID-19,” in ji ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here