Kare Shugaban Kasa ba Kishin Kasa Bane – Dan Majalisa ga Ministan Yada Labarai

 

Honarabul Ben Igbakpa, mamba a majalisar wakilai, ya caccaki ministan yada labarai, Lai Mohammed.

A cewar dan majalisar, kalaman Lai Mohammed na matukar bashi mamaki duk lokacin da ya ke sauraronsa.

Igbakpa ya zargi Lai Mohammed da rashin sanin banbanci tsakanin yada labarai da sharara karya da furta shirme.

Mamba a majalisar wakilai daga mazabar Ethiope, jihar Delta, Honarabul Ben Igbakpa, ya caccaki ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, tare da yin kira gare shi ya daina shararawa ‘yan Nigeria karya yayin gudanar da aikinsa.

Dan majalisar ya bayyana kalaman Lai Mohammed na kare shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin abin kunya.

A cewar dan majalisar, Lai Mohammed “karya kawai ya ke shararawa tare da kara yawan matsalolin gwamnatinsu duk lokacin da ka saurari kalamansa.

Da ya ke magana da jaridar Vanguard a ranar Litinin, dan majalisar bayyana cewa; “ina mamakin yadda jama’a ke manta cewa ba’a dawwama a gwamnati, watarana dole mutum zai bar ofis.

“Na tabbata da ace ba’a cikin gwamnati yake ba shi ma ba zai ke furta irin wadannan Kalaman da yake yi yanzu ba.

“Kare shugaban kasa ba kishin kasa bane, tsayawa tare da sauran jama’a da kundin tsarin mulki shine kishin kasa, amma shi kullum kalamansa na shirme ne da rashin kishin kasa.

“Ba zan manta lokacin da Jonathan ke kan mulki ba, yadda ya dinga caccakarsa, shi yasa yanzu yake borin kunya.

“Ya bar aikinsa na Ministan yada labarai ya koma shugaban yada farfaganda, ya gaza gamsar da ‘yan Nigeria cewa yana yin aikin da aka nada shi; wato sanar da su gaskiyar al’amuran gwamnati.

“Amma shi a wurin Lai Mohammed, aikin ministan yada labarai shine sharara karya, watakila saboda babu wani abu da zai nuna wanda gwamnatinsu ta yi wa kasa,” a cewar dan majalisar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here