Amurka na Korarin Kawo Karshen ‘Yan Ta’addan Najeriya
Kasar Amurka ta ce za ta taimakawa Najeriya da sauran kasashen yammacin Afrika domin yakar ‘yan ta’adda.
Mike Pompeo, sakataren gwamnatin kasar Amurka, ne ya fadi hakan a ranar Laraba.
A kwanakin baya ne dakarun sojin Amurka na tawagar ‘SEAL’ suka dirar wa ‘yan bindiga a arewacin Najeriya a atisayen ceton wani Ba’Amurke Sakataren gwamnatin ƙasar Amurka, Mike Pompeo, a ranar laraba, ya ce ƙasar Amurka zata yi amfani da dukkan makaman da take dasu don yaƙar ta’addanci a Najeriya da yammacin Afirika.
Pompeo ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da haɗakar kasashen duniya (GCD) don cin galabar ƙungiyar ISIS wanda ƙasar Najeriya ta kasance mai masaukin baƙi.
Acewarsa, An samu gagarumar nasara a tattaunawar ganawa da gwamnatin Najeriya.
Read Also:
Sakataren na gwamnatin Amurka ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa; “an samu gagarumar matsaya da nasara a tattaunawa da gwamnatin Najeriya a taron haɗakar ƙasashen duniya don cin galabar ISIS da makamantan ƙungiyoyi irinta a ko ina a faɗin duniya.Ina godiya ga Najeriya da ta ɗauki nauyinn taron.”
A taron, Ƙasar Amurka da takwarorinta, ƙasashe 82, mambobin haɗakar kasashen sun nuna zummar son ganin an kawo ƙarshen ISIS, Boko Haram da sauran manyan ƙungiyoyin ƴan ta’adda na duniya.
Jaridar Punch ta rawaito Kwamandan sashen atisaye na musamman na sojin Amurka a nahiyar Afrika, Manjo Janar Dagvin Anderson, ya na cewa Ƙungiyar ISIS da Al-Qaeda na mamaye a arewacin Najeriya da wasu bangarorin yammacin Afrika.
Arewacin Najeriya na fama da kalubalen tsaro da suka hada da yakin Boko Haram a arewa maso gabas, matsalar ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, da matsalar rikicin manoma da makiyaya a arewa ta tsakiya.
Duk da irin kudi da gwamnati ke kashewa don shawo kan matsalolin, har yanzu ‘sun ki ci, sun ki cinyewa’, lamarin da wasu ke ganin ya kamata gwamnatin Najeriya ta nemi tallafi daga manyan kasashen duniya.