Tinubu ya Maida Martani Akan Dakatar da Fansho da Sanwo-Olu ya yi

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya yaba wa gwamnan jihar legas, Sanwo-Olu a kan kasafinsa na 2021.

Dama gwamna Sanwo-Olu ya bukaci a dakile biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fansho.

A cewar Tinubu, yin hakan almubazzaranci ne, yana tare da Sanwo-Olu dari bisa dari a kan wannan matakin Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya taya gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, murna a kan shirinsa na dakatar da ba wa gwamnoni da mataimakansu fansho, a matsayin matakan dakile almubazzaranci.

A wata wallafa da Tinubu yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Laraba, ya ce:

“Ina taya Gwamna Sanwo-Olu murna a kan kasafin da ya tsara, wanda dama hakan yayi daidai. Wannan kasafin zai taimaki mutanen jihar Legas, sannan zai taimaka wurin bunkasa jihar.”

“Ina so in shawarci gwamnan da yayi gaggawar dakile fanshon gwamnoni da mataimakansu,” cewar Tinubu.

Ya kara da cewa, “Ina matukar farin ciki da wannan matakin da gwamnan ya dauka, ina tare da shi dari bisa dari. Ina shawartar duk wasu ‘yan jam’iyyar APC da suyi koyi dashi.”

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamna Sanwo-Olu ya nemi a rushe biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fansho a cikin kasafin 2021, don yin hakan almubazzaranci ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here