Mambobin Jam’iyyar APC za su Ci gaba da Habaka Saboda Ci gaban da Shugaba Buhari ya Samu – Sen. George Akume
Jigo a jam’iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa ake ganin jam’iyyar APC na kara habaka a kullum sabanin raguwa.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin wani jigo a jihar benue, wanda ya shigo jam’iyyar ta APC.
Ya kuma bayyana cewa, ci gaban jam’iyyar APC na da nasaba ta kai tsaye da ci gaban da Buhari ya kawo.
Jihar Benue – Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sen. George Akume, ya ce mambobin jam’iyyar APC za su ci gaba da habaka saboda ci gaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu.
Read Also:
Akume ya bayyana haka ne a ranar Talata a garin Igbor da ke karamar hukumar Gwer a jihar Benue a lokacin da yake jawabi ga Amb. Yonov Agah, Darakta-Janar na Majalisar Tattaunawar Kasuwanci ta Najeriya da wasu mutane, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ministan ya ce Buhari ya taka rawar gani don haka ne ma mutanen da ba su da sha’awar siyasa ke fitowa a dandazonsu domin shiga jam’iyyar APC.
Ya ci gaba da cewa, jam’iyyar tana kuma karbar ‘yan wasu jam’iyyun siyasa da suke sauya sheka a kullum.
Ya kara da cewa:
“Za mu je garin Daudu da ke karamar hukumar Guma a Benue domin halartar bikin sauya sheka za zarar na kammala jawabina a nan.
“Muna danganta wannan gagarumin sauya sheka ga ci gaban da gwamnatin Buhari ta samu.”
Ya zayyana wasu daga cikin ayyukan ci gaba na gwamnatin Buhari a Benue da suka hada da hanyar Makurdi-Abuja, hanyar Adoka-Naka-Makurdi, da kuma asibitin yara da haihuwa da ke Makurdi, da dai sauransu.
Ya kuma baiwa sabbin masu shigowa jam’iyyar tabbacin samun dama ba tare da la’akari da lokacin da suka zo jam’iyyar ba.