Gwamna Ganduje ya Amince da Murabus Din Kwamishinoni 7 Cikinsu 11

Akalla mutum 11 cikin kwamishanonin gwamnatin jihar Kano sun ajiye aikinsu makon da ya gabata.

Gwamnan jihar ya amince da murabus din mutum bakwai cikinsu kuma yace sauran su koma bakin aikinsu.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ke da niyyar siyasa su ajiye mukaminsu bisa doka.

KAno- Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da murabus din kwamishanoni shida cikin kwamishanoninsa da suka yi murabus don takarar kujerar siyasa a 2023.

Wannan ya bayyana na jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022.

A jawabin, gwamnan ya amince da na mutum bakwai cikin 11 da sukayi murabus, yace guda shida su koma bakin aiki.

Yace:

“An umurci shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da duka sauran kwamishanonin ku koma bakin aiki a ma’aikatunsu.”

Legit ta tattaro muku jerinsu:

1. Hon. Sanusi Said Kiru – Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano

2. Nura Dankadai – Kwamishinan kasafin kudi

3. Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa – Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano zai yi takarar Kujerar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kunchi/ Tsanyawa a Jamiyyar APC

4. Dr. Ali Haruna Makoda – Shugaban Maaikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano zai yi takara a Jamiyyar APC.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here