APC na Ganin Jonathan Zai Kai ta ga ci Idan ya yi Takarar Shugaban Kasa a 2023

 

Ana ta rade-radin APC tana zarwacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Jam’iyyar na tunanin Jonathan zai kai ta ga ci idan ya yi takarar shugaban kasa.

Idan hakar APC ta cin ma ruwa, za a sake mika wa ‘Dan Arewa mulki ne a 2027.

Masu fashin bakin siyasa sun kawo dalilan da suka jawo jam’iyyar APC mai mulki take harin tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan.

Daily Trust tace tun a Nuwamban 2020 ake ganin APC ta na kokarin ganin Goodluck Jonathan ya yi watsi da jam’iyyar PDP ya hada-kai da ita a 2023.

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni yana kokarin karya kafar PDP. Kawo yanzu ya karbe jahohi uku daga hannun ‘yan adawa.

Majiyar APC ta shaida wa jaridar cewa an nemi Dr. Jonathan ya sauya-sheka daga PDP, domin a ba shi tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Wa’adi 1 ya rage wa Jonathan

Dabarar yin hakan shi ne Jonathan ya kawo wa APC nasara a zaben da za ayi a 2023, sai ya yi shekaru hudu a mulki, sai mulki ya koma wa Arewa.

“Lissafin ‘yan Arewa ne domin su cigaba da mulki na tsawon lokaci. Amma batun kai mulki zuwa Kudancin Najeriya a 2023 yana kara karfi.”

“Suna so suyi amfani da Goodluck Jonathan a matsayin jirgin da za su tsallake babban rafi.

Arewa za su yi 10, Kudu sun yi 14

A cewarsa, ‘yan Arewa suna ganin cewa tun da aka dawo mulkin farar hula a 1999 ba su mori shugabanci da kyau ba, don haka suke wannan shiri.

“Obasanjo ya yi shekaru takwas, mulki ya koma Arewa, amma ‘Yar’adua bai kammala wa’adinsa ba. Jonathan ya karasa, kuma ya yi sabon wa’adinsa.”

Har ila yau, wata majiya daga PDP ta bayyana cewa ana ganin Jonathan zai yi dadin tallata wa domin takararsa za ta kawo zaman lafiya a siyasar kasar.

Amma irinsu Jackson Lekan Ojo suna mamakin yadda APC ke neman wanda ta gama yi wa kaca-kaca.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here