APC ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi na Mazaɓar Lere a Majalisar Wakilan Tarayya
INEC ta bayyana sakamakon cike gurbi na mazaɓar Lere a majalisar wakilan tarayya.
Wannan ya biyo bayan rasuwar tsohon ɗan majalisar, wanda ya rasa rayuwarsa a watan Afrilun da ya gabata.
INEC ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Ahmed Mannir, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Kaduna – Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana Ahmed Mannir, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazaɓar Lere a majalisar wakilan tarayya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen a Saminaka ranar Lahaɗi, baturen zaɓe, Farfesa Adamu Wada, yace Mannir ya samu kuri’u 34,958.
Baturen zaɓen yace:
Read Also:
“Mannir na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 34,958 inda ya lallasa abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Ibrahim Usman, wanda ya samu kuri’u 16,271.”
“Salihi Abdulkarin na jam’iyyar YPP ya samu kuri’u 295, yayin da Suleiman Lere na jam’iyyar PRP ya samu kuri’u 226.
“Jam’iyyar APGA wadda bata tsayar da ɗan takara ba a zaɓen, ta samu kuri’u 125.”
Meyasa aka shirya zaɓen cike gurbin?
Zaɓen ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Lere a majalisar wakilan tarayya, ya gudana ne domin cike gurbin ɗan majalisar, wanda ya rasu a watan Afrilu.
Marigayi Suleiman Lere ya rasu ne bayan fama da wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba ranar 6 ga watan Afrilu, kamar yadda punch ta ruwaito.
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya rantsar da shi a watan Maris, duk kuwa da ya nemi takarar kujerar a zaɓen 2019.
Wannan ya biyo bayan kotun ɗaukaka kara da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe, tare da cire ɗan takarar PDP, Lawal Adamu, waɓda yake kan kujerar da farko.