Jam’iyyar APC na Kokarin Ganin ta ci Gaba da Mulki a Kalla na Tsawon Shekaru 32 – Gwamnan Jahar Yobe

 

Gwamnan jahar Yobe ya bayyana manufar jam’iyyar APC ta kasan cewa a mulki har shekaru 32.

Ya bayyana cewa, jam’iyyar na da shirin da zai sa ta zauna daram a karagar mulki na wa’adi da yawa.

Ya kuma jaddada manufar jam’iyyar na ci gaba da samar da romon dimokradiyya ga ‘yan Najeriya.

Shugaban riko na kwamitin tsare-tsaren babban taron kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyar na kokarin ganin ta ci gaba da mulki a kalla na tsawon shekaru 32, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Buni ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin tuntuba da dabaru na jam’iyyar na mambobi 61, a Sakatariyar APC ta Kasa, da ke Abuja, a ranar Talata.

A cewarsa, ya kamata jam’iyyar ta kasance a kan mulki don ci gaba da samar da romon dimokiradiyya da take gabatarwa tun daga shekarar 2015.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke shawarar kafa kwamiti mai karfin gaske don tsara dabaru da shiri tsaf don aiwatar da wannan manufar.

Gwamnan ya ce, “Don haka kundin tsarin dabaru da tuntuba, shi ne ya karfafa nasarorin da muka samu wajen gina jam’iyya mai karfi tare da ingantaccen tsari wanda zai cika APC don fuskantar kowacce jarabawa a kowane lokaci.

“Burinmu shi ne samar da wata dabarar da za ta tsayar da jam’iyyar daram har ta wuce wa’adi na 6, 7 da ma 8 na mulki don aiwatar da manufofin jam’iyya yadda ya kamata, inganta rayuwar ‘yan Najeriya da kuma, ci gaba da kasancewa jam’iyyar siyasa ta Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here