Sojojin Najeriya Sun Bankado Wata Haramtacciyar Matatar Man Fetur Dake Aiki a Jahar Abia

 

Sojojin Najeriya sun bankado wata haramtacciyar matatar man fetur dake aiki a jahar Abia.

Sojojin sun afkawa matatar, yayin da suka lalata ta suka kuma fatattaki ma’aikatanta a cikinta.

Sun samu nasarar kwato motoci da wasu kayayyakin aikin tace danyen man fetur a matatar Mazajen runduna ta 14 ta sojojin Najeriya a Ohafia da ke hade da hedikwatar bataliya ta 144 a karamar hukumar Ukwa ta Yamma ta jahar Abia sun lalata haramtacciyar matatar mai da ke Ukwa ta Gabas.

Wakilin jaridar The Nation ya tattaro cewa matattarar matatar tana aiki ne ta wata dabar danyen mai da ke aiki tsakanin Abia da jahar Ribas.

Wasu majiyoyi sun shaida cewa ba wanda aka kama sannan kuma an tabbatar da kwacewa tare da lalata wasu motocin bas kirar L300 biyu, danyen mai da kuma tankokin da ake amfani da su wajen dafa haramtaccen danyen mai da aka sace daga bututun NNPC a yankin.

Majiyar ta bayyana cewa an gudanar da aikin da ya kai ga lalata haramtacciyar matatar ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na DSS a Owaza dake karamar hukumar Ukwa ta Yamma.

Sun kara da cewa; “Mun samu masaniya game da ayyukan haramtacciyar dabar danyen mai da ke aiki tsakanin Abia da Jahar Ribas.

“Daga bayanan da muka samu, mun bi su zuwa ga al’ummar Nkali a cikin jahar Ribas inda muka gano sansaninsu na tace mai ba bisa ka’ida ba.

“Babu wanda aka kama. Wurin yana da damshi. Abin da ya faru shi ne, da farko sun hango mu sai suka tsere kuma saboda wurin yana da damshi, ya ba mu wahalar iya bin su.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here