Jahar Ondo ta yi Rashin Tsohon Dan Majalisa, Akpoebi Lubi 

 

Jahar Ondo ta yi rashin daya daga cikin tsoffin ‘yan majalisar ta, Akpoebi Lubi, sakamakon hatsarin mota.

Lubi ya rasa ran sa ne a ranar Talata, 23 ga Maris, bayan afkuwar abin takaicin.

Kafin rasuwarsa, marigayi dan majalisar ya kasance tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jahar Rahotanni sun kawo cewa Honarabul Akpoebi Lubi, tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jahar Ondo, ya mutu bayan ya yi hatsarin mota.

Hadimin Sanata Nicholas Tofowomo wanda Lubi ya yi aiki a karkashin sa ne ya tabbatar da wannan mummunan lamarin wanda ya faru da yammacin ranar Talata, 23 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.

Har zuwa lokacin mutuwarsa na ba zato ba tsammani, Lubi ya kasance mashawarci na musamman ga Tofowomo kan dabaru da maslaha ta musamman. Kasancewar ya wakilci mazabar Ese-Odo a lokacin gwamnatin Olusegun Mimiko, tsohon dan majalisar ya kasance dan jam’iyyar PDP daya tilo da aka zaba a Majalisar a 2011.

A cewar jaridar Punch, mamacin ya kasance tsohon shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Ese-Odo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here