APC da PDP Sun Kunyata Kasar Nan – Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabiu Kwankwaso ya kara caccakar APC da PDP kan mulkin Najeriya tsawon shekaru 24.
Kwankwaso, mai neman zama shugaban kasa a inuwar NNPP ya fara kamfe gadan-gadan a arewa maso gabas.
Dan takarar ya ce manyan jam’iyyun sun maida kasar nan baya ta kowane bangare, ya shawarci mutane su guje su a 2023.
Bauchi – Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam’iyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci ‘yan Najeriya su guji zaben wasu jam’iyu musamman APC da PDP a zaben watan Fabrairu.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kwankwaso ya baiwa yan Najeriya wannan shawarin ne a wurin Ralin kamfe dinsa na arewa maso gabas da ya gudana a Bauchi.
Kwankwaso ya bayyana cewa akwai bukatar mutanen Najeriya su farga su fatattaki APC da PDP wadanda suka lalata Najeriya tsawon shekaru sama da 20.
A kalamansa, ya ce:
Read Also:
“Bari na yi amfani da wannan damar na gaya maku mutanen arewa maso gabas da ma Najeriya baki daya cewa jam’iyyarmu NNPP wuyanta ya kai tsara, mun shiga kowace gunduma a kasar nan.”
APC da PDP sun kunyata kasar nan – Kwankwaso
Tsohon gwanman jihar Kano ya roki magoya bayan jam’iyyar NNPP su tashi tsaye su yi aiki tukuru domin damin nasara a watan Fabrairu.
A cewarsa, mulkin manyan jam’iyyu biyu watau PDP da APC da ya shafe shekaru 24 ya gaza mafi munin gazawa.
Karidar Ripples Nigeria ta rahoto dan takarar na cewa:
“Sun gaza tsinana komai a kasar nan kama daga bangaren tattalin ariziki, tsaro da manyan ayyukan raya kasa, sun gaza har a bangaren hada kan ‘yan Najeriya.”
Kwankwaso ya ce jam’iyyar NNPP ce kadai mafita game da kalubalen da suka dabaibaye Najeriya sakamakon gurbataccen shugabanci a tsawon waɗan nan shekaru.
Tsohon gwamnan ya ce idan har ‘yan Najeriya suka amince masa, gwamnatinsa zata tsawaita JAMB ta kai shekaru hudu kafin a daina amfani da ita.