Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar ADC ya Kamu da Cutar Corona

 

Mai neman zama shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da cutar Corona .

A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a, Kachikwu ya bayyana cewa ya killace kansa har sai an tabbatar masa da ya warke.

Ya yi kira ga yan Nqjeriya da su ci gaba da bin matakai suna zuwa ana gwada su domin kar a maida hannun agogo baya a Najeriya.

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress, Dumebi Kachikwu, a ranar Jumu’a ya bayyana cewa ya kamu da cutar Covid-19 wato corona.

Mista Kachikwu ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi takatsantsan domin akwai yuwuwar cutar ta sake dawowa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Mai neman kujera lamba daya a Najeriya a inuwar ADC ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a 13 ga watan Janairu, 2023.

A sanarwan, Kachikwu ya bayyana cewa tuni ya killace kansa kuma ya soke duk wasu tarukan al’umma har zuwa lokacin da za’a tabbatar masa ya warke daga cutar.

Ya kuma kara da kira ga mutanen Najeriya karsu dauki lamarin Korona da wasa domin a halin da ake ciki adadin masu kamuwa da ita ya karu a fadin duniya a cikin makonnin nan.

A rahoton Vanguard, Dan takarar shugaban ƙasan ya ce:

“Bai kamata ‘yan Najeriya su jingine matakan kariya ba duk da gwamnati ta sassauta dokokin COVID19, tsarin kula da lafiyarmu ba zai iya daukar yawaitar kamuwa da cutar ba.”

“A yanzu muna wani lakaci da kwararrun likitoci ke barin kasa, ya kamata mu rika zuwa ana gwada mu kuma mu bi matakan dakile yaɗa cutar. Dole mu guje maida ralin kamfe wurin yada korona, kar mu maida hannun agogo baya.”

“Zamu fita daga annobar corona idan har muka natsu kuma muka bi matakan da ya dace.”

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here