Matar Aure Mai Shekaru 8 da Mijinta ta Nemi Kotu ta Raba Auranta

 

Wata matar aure Muhibbat Lawal, mai ‘ya’ya biyu ta shigar da bukatarta gaban kotu na raba aurenta mai shekaru takwas da mijinta, mai cusgunawa mata.

Dalilan da ta gabatarwa kotu sune, karancin soyayya, cin zarafi bainar jama’a da kuma rashin daukar dawainiyarta da yake, kasancewar ya maidata jakarsa da yake jibga kullum.

Sai dai, Lawal bai kalubalanci bukatar raba auren da ta shigar ba, amma ya musanta cin zarafinta a bainar jama’a.

Oyo – Wata mata mai ‘ya’ya biyu, Muhibbat Lawal, a ranar Juma’a ta roki kotun Mapo Grade A dake Ibadan da ta raba aurensu mai shekaru takwas da mijinta mai cusguna mata saboda cin zarafi, karancin soyayya da rashin daukar dawainiyarta da yake.

Kamar yadda ta bayyana, Muhibbat ta ce ta hadu gami da tsunduma kogin soyayyar Lawal ne a kafar sada zumuntar Facebook.

“Bayan bikin aurenmu a anguwan Offa, munanan halayen Lawal suka bayyana karara saboda yadda ya maida ni jakar dukansa. Yana jibgata duk lokacin da na bukaci wani abun amfanin gida.

“A takaice dai, yana zargina da bin maza gami da cin mutuncina gaban kowa.”

– Muhibbat ta shaidawa kotu. A cewarta, tunda yanzu babu soyayya tsakaninta da azzalumin mijinta, kotu ta bata damar raba aurensu, Daily Nigerian ta rahoto.

Lawal, wanda bai ki amincewa da bukatar Muhibbat na raba auren ba, sai dai, ya musanta cin zarafinta a zaman shekaru takwas da suka yi.

Ya shaidawa kotu:

”Ta saku idan hakan take bukata, kuma a shirye nake da in dauki dawainiyar ‘ya’yan.”

Shugabar kotun, S.M Akintayo, ta tsaya kan cewa tunda ta nuna karara bata bukatar cigaba da zama da Lawal a matsayin miji, kotu bata da wani zabi da ya wuce ta biya mata bukatarta na raba aurensu don tabbatar da zaman lafiya.

Alkaliyar ta ba mai karar damar kula da yaran da suka haifa, amma ta umarci wanda ake karar da ya tabbatar da yana biyan N15,000 duk wata na dawainiyarsu.

Haka zalika, Mrs Akintayo ta bada umarnin kange Lawal daga kodai yi mata barazana ko shiga rayuwar Muhibbat.

Sai dai, ta bada umarnin biyun cewa sune ke da alhakin kan karatu da sauran walwalar yaran.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here