2023: Jam’iyyar APC na Tantance ‘Yan Takarar Shugaban ƙasa

 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na tantance masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin tutar jam`iyyar.

Da farko dai jam`iyyar ta tsayar da ranar Talatar da ta gabata a matsayin ranar tantacewar, amma sai ta dage ba tare da bayyana dalili da kuma sabuwar ranar da za ta yi aikin ba.

Ana aikin tantancewar a otal din Transcop Hilton a Abuja

Jumullar mutum 23 ne ake sa ran cewa za su halarci tantancewar.

Rahotanni na cewa ana sa ran tantance mutum 11 a yau Litinin, sannan kuma sauran 12 kuma a gobe Talata.

Wannan duk na zuwa ne bayan da jam’iyar ta APC ta ɗage zaɓen fitar da gwanin da ya kamata ta gudanar 29 da 30 ga watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here