ƙungiyoyin Magoya Bayan APC na ƙasa na kira ga Shugaba Tinubu da ya Maye Gurbin Ministan Kaduna da Kailani Muhammed

 

Gamayyyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa sun hango wanda ya fi dacewa ya zama minista daga Kaduna.

Ƙungiyar ta shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabanta, Alhaji Kailani Muhammed, minista daga jihar Kaduna.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne dai ta hannun darektan watsa labaranta, wanda ya lissafo dalilian da yakamata su sanya a ba Kailani kujerar minista.

FCT, Abuja – Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Darekta Janar ɗinta, Alhaji Kailani Muhammed, a matsayin minista daga jihar Kaduna.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa ta hannun darektan watsai da hulɗa jama’a ɓa ƙungiyar, Dr. Saleh Bin-Ahmed, a birnin tarayya Abuja, ranar Talata, 12 ga watan Satumba, cewar rahoton NAN.

Shugaban ƙasa Tinubu dai ya zaɓi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista daga Kaduna, amma majalisar dattawa ta ƙi amincewa da shi bisa rahoton tsaron da aka gabatar a kansa.

Dalilan ƙungiyar na neman a naɗa Kailani minista

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar APC na ƙasa na kira ga shugaban ƙasan mu Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin ministan Kaduna da shugaban ƙungiyar, Injiniya Kailani Muhammed.”

“Wannan shi ne dalilan da zai sanya APC ta sake komawa mulki cikin sauƙi a shekarar 2027, bisa cewa an biya ƙungiyoyin goyon baya wahalar da suka sha kuma an dama da su a gwamnati.”

A cewar Bin-Ahmed, Kailani haziƙin ɗan siyasa ne mai taimakon jama’a wanda ya ƙware a aikin gwamnati, gogaggen ɗan jarida, mai sharhi kan al’amuran jama’a, sannan uwa uba kuma mai samar da sabbin ra’ayoyi.

“Yana da abin da ake buƙata domin samar da romon dimokuraɗiyya ga ƴan Najeriya.”A cewarsa.

“Muna fatan cewa Shugaba Tinubu zai yi duba da idon basira kan kiraye-kirayen da al’umma ke yi, domin babu wani lokaci wanda ya wuce na yanzu.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com