Rema ya Lashe Kyautar Waka Mafi Shahara a Salon ‘Afrobeats’

 

Matashin mawaki a Najeriya wanda ke tashe, Rema ya lashe kyautar waka mafi shahara a salon ‘Afrobeats’ saboda wakarsa mai suna ‘Calm Down’ a bukin karamma mawaka na MTV Video Music Awards.

Ya doke sauran manyan mawaka a Najeriya irinsu Burna Boy, Davido, Wizkid, Fire Boy da kuma Ayra Starr domin lashe wannan kyautar a ranar Talata.

Kawo yanzu an saurari wakar ‘Calm Down’ fiye da sau biliyan daya a manhajar Spotify.

An gudanar da bikinne a Newark da ke New Jersey a Amurka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com