Badakalar N7trn: Ana Binciken Mutanen da ke da Alaka da Emefiele

 

Abuja – Watakila nan da ‘yan kwanaki kadan mutanen Najeriya su ji labarin badakalar da za ta shiga cikin mafi girma a tarihin kasar nan.

Wani rahoton The Guardian ya bayyana cewa kwamitin bincike na musamman da aka kafa domin ayyukan bankin CBN ya tono babban aiki.

Wannan kwamiti ya kama hanyar bankado wasu da ake zargi su na da hannu a satar kudin da adadinsu zai iya kai Naira tiriliyan bakwai.

Kwamitin Jim Obazee ya na da hurumin binciken abubuwan da su ka faru a CBN – bankin da ke alhakin kula da duk harkokin kudi a doka.

Idan kwamitin ya kammala aikinsa, za a san gaskiyar duk abubuwan da su ka faru a lokacin da Godwin Emefiele yake rike da bankin CBN.

Godwin Emefiele ya jagoranci bankin na tsawon shekaru tara, tun bayan da Goodluck Jonathan ya tsige Sanusi Lamido Sanusi a tsakiyar 2014.

Rahoton da aka samu ya ce yanzu haka ana duba takardu, bayanai da kalaman da aka samu a bankin, kuma za a iya cafko wasu mutanen dabam.

Duk da ba a tabbatar da gaskiyar zancen ba, ana cewa kwamitin Obazee zai binciki wasu jakadun Najeriya da ke kasar Larabawa a kan zargin.

Wasu manya da ke kasashen ketare sun yi kokarin ba abubuwan da su ka faru a CBN daurin gindi.

Alamu na nuna za a shiga bankunan kasashen ketare domin fadada binciken badakalar satar da ake zargin an tafka ta karkashin CBN,

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com