Jihohin Arewa Maso Gabashin Najeriya da za su Samu Ruwan Sama Mai Karfin Gaske 

 

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun ruwan sama mai karfi gaske da tsawa a wasu sassa na arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar, Muntari Ibrahim ne ya shaida haka a sanarwar da ya fitar.

A cewarsa, jihohin da za su fuskanci wannan yanayi sun hada da Borno da Adamawa da Gombe da kuma Taraba.

Sannan sanarwar ta kuma ce za a samu ruwa tafe da iska a jihohi irinsu Gombe da Bauchi da Benue da Filato da Nasarawa da Enugu da Ebonyi.

Sai wasu kuma jihohin kudanci. Rahoton ya ce za a shafe tsawon sa’a uku zuwa shida ana tafka ruwan.

Nimet ta shawarci mutane suyi takatsan-tsan da kasancewa masu kula saboda tsaronsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here