Arsenal,Real Madrid da Atletico Madrid na Zawarcin Adrien Rabiot

 

West Ham na gab da sayan ‘yan wasa biyu wadanda suka hada da mai kai wa Borussia Dortmund hari da Jamus Nicolas Fullkrug, mai shekara 31, da dan wasan gaban Leeds da Netherlands Crysencio Summerville, dan shekara 22. (Sky Sports), external

Arsenal da Real Madrid da Atletico Madrid duk suna zawarcin dan wasan tsakiyar Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 29 wanda ba shi da kungiyar da zai taka wa leda bayan ya bar Juventus. (Gazzetta, in Italian), external

Aston Villa ta cimma matsaya da Chelsea kan dan wasa mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku, sai dai dan wasan mai shekara 31 na son ya koma Kungiyar Napoli ta Antonio Conte. (Il Mattino, in Italian – subscription needed), external

West Ham ta amince ta sayi dan wasan baya ta gefen dama Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 26, amma har yanzu ba ta cimma matsaya da Manchester United a kan kudin da za ta biya ba. Man U dai na son a biyata fam miliyan 18 a maimakon fam miliyon goma. (Sky Sports Germany), external.

Fulham na tattaunawa da Villarreal domin daukar dan wasan tsakiyar baya na Sfaniya Jorge Cuenca,mai shekara 24, a kan fam miliyan 6.7. (Standard), external

Napoli na shirin yi wa dan wasan tsakiyar Brighton da Scotland Billy Gilmour dan shekara 23 tayin yuro Miliyan 12 kuma ta na jiran ficewar wasu ‘yan wasa kafin ta yi masa wannan tayi. (Sky Sports Italy), external

Arsenal na gab da kulla yarjejeniyar fam miliyan 25 domin sayan dan wasan tsakiyar Sfaniya Mikel Merino mai shekara 28 daga Real Sociedad. (Mirror), external

Roma ta cimma matsaya da Girona domin sayan dan wasa mai kai hari na Ukraine Artem Dovbyk, mai shekara 27, a kan fam miliyan 28.8m yayin da AC Milan na son ta sayi dan wasan gaban Roma da Ingila ammy Abraham, mai shekara 26. (Repubblica, in Italian – subscription needed), external

Stuttgart za ta janye zawarcin da take yi wa dan wasa mai kai hari na Brighton da Jamus Deniz Undav, mai shekara 28, kuma za ta maida hankali a kan wasu ‘yan wasa idan ta kasa cimma matsaya da Albion. (Kicker, in German), external

Newcastle na tattaunawa da Sheffield United domin daukar dan wasa mai kai wa Blades hari da kuma Denmark, William Osula mai shekara 20 a kan kudi fam miliyan 29. (Telegraph – subscription needed), external

Leipzig za ta yi watsi da tayi na biyu da Barcelona ta yi mata akan dan wasan tsakiyar Sfaniya Dani Olmo mai shekara 26. (Sport, in Spanish), external

Bristol City da Stoke da Birmingham City na sha’awar dan wasan mai tsaron baya na Burnley da kuma Ireland Luke McNally, dan shekara 24. (Football Insider), external

Stoke City na son dan wasan tsakiyar Blackburn Rovers da Ingila Lewis Travis, mai shekara 26. (Teamtalk), external

Nottingham Forest ba ta da anniyar cefanar da dan wasan tsakiyar Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 24 duk da zawarcin da Newcastle da Arsenal da Aston Villa da kuma Chelsea su ke yi masa. (HITC), external

Dan wasan tsakiyar Manchester City da Ingila Jacob Wright, dan shekara 18, ya amince a bada shi aro ga Peterborough United. (Football Insider), external

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here