#EndSARS: Dalilin Dayasa Na Goyi Bayan Zanga-Zangar da Aka yi a Arewacin Najeriya: Fitaccen Mawakin Hausa, Nazifi Asnani
Sunan Nazifi Asnanic a masana’antar shirya Fina Finai ta Kannywood da rera wakoki bashi da bukatar doguwar gabatarwa bare nanatawa,domin kuwa sanannne ne,kana fitacce kuma kwararre.
Mawakin Wanda alkiblar wakokin sa sunfi duba madubin dubaradun al’amuran rayuwa,da zamantakewar yau da kullum ya samu zaren zarafin tattaunawa da Hannatu Suleiman Abba, Zainab Nasir Ahmad, Amina Adam Yusuf,da Mohammed Dahiru Lawal dukkanin su daga Jaridar Arewa Agenda, a inda ya zayyane tare da fayyace dalilan da na fara waka tunda fari, musabbabin goyon bayansa ga zanga zanga ta Arewacin Nigeria, ra’ayin sa game da salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari, harkar tsaro da sauran al’amura dake ci wa kasa tuwo a kwarya musammman a Arewacin Nigeria.
AREWA AGENDA: Da farko zaka iya gaya mana waye Nazifi Asnanic?
ASNANIC: Sunana Nazifi Abdulsalam Yusuf wanda aka fi sani da Nazifi Asnanic. Mawaki ne ni kuma ma rubucin waka daban daban kamar wakan siyasa, film dadai sauran su. A takaice dai ni mawakine.
AREWE AGENDA: Meya ja ra’ayin ka cikin waka kuma gashi har hayi suna dashi?
ASNANIC: A gaskiya fahimta nayi cewar ta hanyar waka zan iya aikawa da sakonnina duk inda nake so su je. A gaskiya waka hanya ce ta isar da sako ba a iya inda kake ba har duniya ga baki daya. Wannan yasa na shiga waka sai kuma Allah yasa aka karbi wakar ta mu.
AREWA AGENDA: Da farawar wakar ka, akwai wakan daka taba yi har aka samu sauyi?
ASNANIC: Alhamdulillahi akwai waka mai suna ‘Dawo Dawo’ wanda ya kawo sauyi a siyasar Kano da kuma a fanin fakakarwa akwai waka mai suna ‘Dije’ wanda nayi da aboki na Ali Jita akan karatun mata kuma gaskiya wannan wakar tayi tasiri sosai.
AREWA AGENDA: Masha Allah, yanzu dai muna iya cewa kai cikaken dan kannywood ne Kenan?
Asnanic: Gaskiya.
AREWA AGENDA: To ya zaman Kannywood take yanzu a matsayin tana film industry?
ASNANIC: Idan akace kannywood wajene wanda ya kunshi mawaka da yan film, so muna iya cewa kannywood wuri ne na sana’a wanda zaka samu abun cin abinci a cikin ta. Da farko dai ana fama da matsalar piracy amma Allah ya kawo sauki saboda an shiga zamani da ake streaming da kuma marketing online. Ana fama da matsalar haryanzu amma an samu sauki sosai saboda wannan zamani da kuma taimakon gwamnati.
AREWA AGENDA: A kwanakin nan duba da matsalar da muka tsinci kanmu a ciki sati biyu da suka wuce an ganka cikin tawagar wadanda suka fito nuna kishin kai musamman abin da shafi arewa. Shin zaka iya gaya mana mesaya ka shiga wannan tawagar?
ASNANIC: To ai tunda inda dan arewa ya kamata in fito saboda ba wani dalilin da bazanyi kishin arewa ba. Gaskiya ni nationalist ne saboda bana jin a akwai wata kasa wanda zanji nafi jin dadin sa sama da Najiriya, a Najiriyar ma arewa saboda nan na tashi aka bani tarbiya da iya karatun da za’a iya bani a gidan mu so in na kalli wadanda basu da wannan abu bani jin dadi shi yasa dole ne in fito in nuna ina kishin arewa idan abin ya shafi arewa. Abin bakin ciki shine idan kai kana nuna kishi wadanda ya kamata sununa support sai su zo suna dakileka, misali mun fito zamuyi wani tattaki sai aka hanamu kuma iyan arewa ne sai kaga wai shin kai kadai kake kishin arewan koko kai kafi kishin saboda yan arewa ne suka hana mu.
AREWA AGENDA: Me zakace gami da abubuwan da suka shafi arewa yanzu?
Read Also:
ASNANIC: Gaskiya abubuwan da suke faruwa yanzu sai dai a bar wa Allah, abin da yasa nace haka idan matsifa irin wannan ta zoma sai dai ka koma ga Allah. Muna cikin yanayi mai bukatar addu’a sossai. Idan mun ce zamu jira gwamnati to bamu shiryaba. Kamar yanda shugaban kasa ya taba fadi “change begins with me” to dolle mu yarda da wannan inaga in mu rike wannan Allah zai kawo mana sauki danko Shi Allah yace “tashi in taimake ka”.
AREWA AGENDA: Ya magamin siyasar ka fa? Da dama ana dangantaka da Senetar Rabiu Musa Kwamkwaso wasu kuma suna ganin kamar tun daga sama kanada wani bangare. Shin me gaskiyar al’amarin?
ASNANIC: Tunda nake dan kasa kuma a lokacin democradiyya yakamata ace nima ina taka rawa a bangaren siyasa, idan nace bana siyasa kamar wani abune nayi na cutar kai tunda inada magoya baya. Da gaske ne ina tare da Rabiu Musa Kwankwaso saboda wasu halaye da dabi’un sa. Kamar yanda kika ce duk wanda daya sanni ya san nayi tafiyar Buhari dan nayi masa kyekkyawan zato bama niba duk wandake kasar yayi mai zato na alkhairi, so inya chanja dama dan Adam ne akwai yuwar hakan.
AREWA AGENDA: Dangane da matasa, akwai wani kalubale ko nasara da kake gani matasa na dashi nan gaba?
ASNANIC: Matasa sune kashin gadon bayan al’uma gabaki daya. Yanzu in zan tara matasa na arewa in fadi wata magana za kuyi mamaki saboda matasan idan da zamu tsaya mu yarda muce mu matasa mun amsa zamu iya yin abinda na sama basuyi ba ko da an sha mamaki, amma su matsan basu so sun fi gane wa su fita Nigeria su sauki kaya su zo su sayarda. So in matasa basu shiga siyasa ba akwai kalobali mai karfi nan gaba ma ba yanzu ba.
AREWA AGENDA: Kamar yanzu a industry din (kannywood) ta yaya keke ganin karuwar mata, kuma koda akwai wata nasara ko cigaba da suke kawowa saboda samun sauya tunani ga shigar su industry din?
ASNANIC: Kin kawo magana wanda a harde take saboda na farko me yasa suke shiga industry din? Wasu sun shigo saboda talauci, waso saboda sun kasa zaman aure sukaga cewa a industry din zaso samu kwanciyar hankali kuma ta zo ta bada gudumawa. Da ace industry din zata yi amfani da labarin su wajen fadakar da jama’a to da za a samu cigaba.
AREWA AGENDA: Shin akwai kira da akeyi wa shugabanni musamman na bangaren arewa nakan cewa a zo ayi wani abu da zai kawowa arewa cigaba musamman ta muka?
ASNANIC: Tabbas anayi, kawai abin da ake cewa shine idan anyi Allah yasa su ji kiran. Dan babban matsalar shine za ayi kiran sun ji amma kuma sai ayi watsi dashi.
AREWA AGENDA: A matsayin ka na matashi kuma sananne wani irin kira zakayi wa yan uwanka wato celebrities domin ganin cewa sun amfani da muryar su dan ganin cewa an samu sauyi a Nigeria musamman a Arewa.
ASNANIC: Gaskiya ne wannan yanada amfani. Kamar yanda na ce matasa iri nane suka fi yawa a industry din musamman a bangaren waka, dama mu daure muyi waka irin yanda muke yin na soyayya muyi a kana abin dake damun arewa inaga in Allah ya yarda abubuwa zasu chanza. Nayi wannan kira kuma Allah yasa zai je gare su.
AREWA AGENDA: Cikin irin wakokin da kake yi wani iri kafi jin dadin yi kuma saboda me?
ASNANIC: Ba bangaren da ban jin dadin sa saboda ni idan zanyi kwaina da zakara nakeyi. Kawai idan yanzi aiki juyawa nakeyi bangaren.
AREWA AGENDA: Yaya kake ganin harkar waka nan da shekara goma masu zuwa musamman a arewa kuma meye burin ka akanta?
ASNANIC: In dai buri nane nan da shekara goma zan so ace yanda za a yi rubutu a kan wakar fadakarwa ta danne ta soyayya. Haka nake son ganin wannan lokacin kuma in Allah ya yarda yanda nake ganin mawaka hankalin su ya fara komawa wajen.
Arewa Agenda: Wani tanadi kukeyiwa mawaka masu tasowa musamman ku da kuka riga kukayi suna?
ASNANIC: Kullum yanda muke cewa shine kada mawaka masu tashi suce sai wakar soyayya zasuyi. Suyi bincike suga akwai sauran irin wakokin da in sunyi zasuyi nasara.
AREWA AGENDA: munji ra’ayin ka yanzu zamu dawo wani bangare. Wani abinci ne kafi so?
Asnanic: Kamar kullum yanda nake fada abinci na guda biyu ne, sune Alkubus da kuma wake da shinkafa saboda ni dan gargajiya ne.
AREWA AGENDA: Menene hobby din ka?
ASNANIC: Hobby dina shine sports musamman table tennis da kwallon kafa.
AREWA AGENDA: Wane kala kafi so?
ASNANIC: Green nafi so.
AREWA AGENDA: To mun gode sosai.