Zulum: Ka Cancanci Yabo a Gurin Kowa

 

Masu ta’aziyya a gida da waje sun yi alhinin kisan manoma 47 a Zabarmari, jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kisan wadannan manoma.

Yau mako daya da rashin wadannan mutane da aka raba iyalansu.

Kisan akalla manoma akalla 47 a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, ya sake jaddada kiran da mutane ke yi na shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro.

Hakazalika wasu sun yi kira da shugaban kasa yayi murabus saboda tabarbarewan tsaro.

Amma yayinda jama’a ke cigaba da tsokaci kan lamari, gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sha ruwan addu’o’i bisa irin abubuwan da yayi lokacin jana’izar mamatan.

A bidiyon da ya yadu a kafafen ra’ayi da sada zumunta, an ga gwamnan cikin jama’a ana birne mamatan tare da shi duk da matsayinsa na gwamna.

An ga Zulum yana kwaba kasa yana zubawa kan kabarin mamatan.

Gwamnan ya cika da hawaye da damuwa kuma yayi maganganu masu ratsa zuciya kan abinda ya kamata gwamnatin tarayya tayi don kare rayukan jama’a a kasar nan.

buy guest posting

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here