Gwamnatin Zamfara Tayi Kalamu Masu Zafi ga Tsohuwar Gwamnatin Jahar

Za’a yi zaben yan majalisun jaha domin maye gibin wadanda suka mutu.

Cikin zabukan da za’ayi a jahohi daban-daban a fadin tarayya, akwai daya a jahar Zamfara.

Yan takara 14 zaku kara gobe domin lashe kujerar dan majalisan mazabar Bakura.

Gwamnan jahar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle, ranar Juma’a ya gargadi gwamnonin APC biyar da Sanatoci bakwai da tsohon gwamna Yari ya gayyata su nisanta kansu daga jiharsa.

Matawalle ya bayyana hakan yayinda ake shirin zaben yan majalisa ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya yi wannan gargadi ne bayan duba dukiyan da yan daba suka lalata yayin yakin neman zabe ranar Alhamis.

“Idan tsohon gwamna Yari dan halas ne kuma haifaffen iyayensa, ya fadawa mutanensa su nisanta kansu daga zaben ranar Asabar a jahar.

Kuma idan ya cika jarumi, ya fuskanceni. Zan lallasa shi,” yayi gargadi.

“Ya gayyaci gwamnoni biyar, Sanatoci bakwai da yan majalisa gooma, har da Ministan harkokin yan sanda Zamfara don tayashi lashe zabe.”

“Irinsu Ministan harkokin yan sanda batawa shugaba Muhammadu Buhari suna sukeyi.”

“Ya gayyato yan daba suna tayar da hankulan mutanenmu har aka kashe biyu kuma aka lalata wuraren yakin neman zabenmu da dukiyoyin mutane.

“Ina gargadin wadannan gwamnoni cewa jahar Zamfara daban take kuma su cire kansu daga lamuranmu. Su bari mutane su zabi wanda suke so.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here