Shin Wai Yaushe  Kungiyar ASUU Zata Janye Yajin Aiki ?

Shugaban ASUU ya ce ba za su janye yajin aikinsu ba sai gwamnati ta biya su albashin da ta rike.

Ya ce babu yadda za a yi malamai su koma makarantu cikin yunwa da rashin kudi, a ranar Lahadi.

Farfesa Biodun Ogunyemi, ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai da yayi ta waya.

ASUU ta ce ba za ta janye yajin aikinta ba har sai gwamnati ta biya duk mambobinta albashinsu da ta rike, The Punch ta wallafa.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ta waya a Legas, ya ce matsawar gwamnati bata biya malamai albashinsu da ta rike ba, ba za su koma makarantu ba.

Idan ba a manta ba, akwai wasu rahotonnin na 27 ga watan Nuwamba, wadanda kungiyar ta amince da janye yajin aikinta saboda gwamnati ta yarje da biyanta naira biliyan 70.

Amma a ranar Lahadi, Ogunyemi ya bayyana cewa sai gwamnati ta biya mambobin kungiyar tsaf, tukunna za ta yanke shawara ta koma.

A cewarsa, “Har yanzu muna ta tuntubarsu, zuwa karshen sati za mu yi rahoto. Sai gwamnati ta biya albashin wadanda ta rike tukunna za mu koma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here