ASUU: An Kokarin Raba Mu da Mutanen Mu
Ana nema shiga wata na goma tun bayan da kungiyar ASUU ta malaman jam’o’i ta fara yajin aiki.
Duk wani kokari na sulhunta sabanin da ya shiga tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya bai tasiri ba.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce sai jami’o’i masu zaman kansu da kasashen keatare sai tsince mambobinsu suke yi.
Shugaban ƙungiyar malaman makarantun jami’a na Najeria; ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, a ranar Alhamis, ya ce suna rasa malamai mambobin ƙungiyarsu sanadiyyar gazawa da halin ko in kula da gwamnatin tarayya take nunawa don ɓiyan buƙatun ƙungiyar.
Da yake magana a wata hirar talabijin wadda jaridar The Punch ta jagoranta, Farfesa Ogunyemi ya ce gwamnati ba zata yi musu barazana da kai ƙararsu ko kuma ɗaukar matakin kotu ba.
Ya ce, “maganar da suke wai suna son zuwa kotu don su tsorata ƙungiyarmu ta saduda ba mai tasiri ba ce.
Ba haka ake yi wa malaman makaranta ba, babu ƙasar da ta zata kai gaci ba tare da malamai ba, muma muna da zaɓin mu.
Read Also:
“Ana maganar kai ya ɗau caji ne yanzu, zan iya sanar da kai a hukumance, malamai 25 a Arewa maso gabas tuni wata jami’a a Yola ta ɗebe su, mun rasa su.
“Mun san mai jami’ar. Wannan shine abin da yake faruwa, jami’o’i masu zaman kansu suna farautar malaman jami’o’i gama gari, saboda sai makarantun gama gari sun gurgunce sannan za su yi tasiri.
“Muna kuma sane da cewa ƙasar Ethiopia sun zo Najeriya sun ɗebi malamai masu mukamin Farfesa guda 200 kuma har yanzu suna neman ƙari. Ban sani ba ko gwamnati tana son ƴansiyasar data naɗa su fara koyarwa da ɗalibai ba.
“Koda yake da yawa daga cikin ƴaƴansu ba makarantun gwamnati suke zuwa ba, shi yasa basu san zafin hakan ba. Malaman dukiyar ƙasarmu ce, ba zamu bari a ƙarar dasu ba.”
Da yake ƙarin bayani, Shugaban na ASUU ya ce zasu tare dukkan wani yunƙuri na gwamnatin tarayya na ƙoƙarin tsawaita gwajin manhajar tsarin UTAS wanda ƙungiyar ASUU ta kawo.
Farfesa Ogunyemi ya ce kamar yadda Ministan ƙwadago, Chris Ngige, ya faɗa, ranar Talata, “za’a ɗauki tsawon sati guda ana gwajin tsarin UTAS, saboda gwamnati tana da wata tantama akan tsarin”.