KADPOLY: Wani Tsohon Malami ya Kashe Matarsa da Kansa

Ana zargin wani tsohon malamin KADPOLY da kashe kansa – Sai da Austin Umera ya harbi matarsa, sannan ya kashe kansa.

Har yanzu ba a gano dalilin da zai sa babban mutum irinsa ya kashe kansa.

ba Wani tsohon malamin KADPOLY, mai suna Austin Umera ya shayar da mutane mamaki a kan abinda ya aikata.

Ana zarginsa da laifin harbin matarsa, Dokta Maurin, wacce ita ma malama ce a jami’ar jihar Kaduna (KASU), inda daga bisani ya harbe kansa kuam ya fadi ya mutu.

Al’amarin ya faru ne a gidansu da ke layin Kigo a cikin garin Kaduna.

Yanzu haka Dokta Maurin tana kwance a asibitin sojoji na 44 da ke cikin Kaduna, inda ake cigaba da kulawa da lafiyarta.

An adana gawar mijinta a ma’adanar gawa dake asibitin kwararru na Barau Dikko a Tudun wada.

Jaridar Daily Trust ta samu labarin wannan mummuna al’amarin ne da misalin karfe 10 na daren Laraba.

Har ila yau, babu cikakke kuma gamsasshen bayani a kan silar aukuwa lamarin amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin

nigerian news up date

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here