Wa’adin Mako Biyu da Shugaba Buhari ya Bayar ya yi Yawa – Shugaban ASUU

 

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ya ce wa’adin mako biyu da shugaban kasar ya bayar domin kawo karshen yajin aikin ya yi yawa.

A wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, shugaban na ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce a bangarensu na malaman jami’a, cikin kwanaki biyu za a iya warware wannan matsala.

Ya kara da cewa ”mako biyu ya yi yawa, an riga an kammala tataunawa domin cimma matsaya, kawai zuwa za ku yi ku ce mana kun amince, wannan kuma ba zai wuce kwana biyu ba”

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce ”A kowacce shekara ‘yan Najeriya na kashe kusan biliyan 200 wajen biyan kudin makaranta a jami’o’in kasar Ghana”

”Ya kamata gwamnati ta bai wa bangare ilimi fifiko a kasar nan, saboda dukkanmu mun je makaranta” in ji Shugaban

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu ne kungiyar ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda sai dai daga baya ƙungiyar ta mayar da yajin aikin na Illa Masha Allahu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here