Kungiyar ASUU za ta yi Zaman Tattaunawa Don Yanke Shawara Kan Dawowa Bakin Aiki
Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kai ruwa rana da kungiyar ASUU don kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Majalisar zartaswar kungiyar ASUU za ta yi zaman tattaunawa don yanke shawari kan dawowa bakin aiki.
Daliban jami’o’in gwamnatin a Najeriya na ci gaba da koka zaman gida da suke yi na tsawon watanni.
FCT, Abuja – Tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar malaman jami’a (ASUU) za ta guda a daren yau a babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton Punch.
Ganawar, wacce manyan kungiyar ta ASUU ce za su tattauna a cikinsa zai kawo shawarin karshe ne kan yiwuwar janye yajin aikin da kungiyar ta dade tana ciki.
Da take zantawa da wakilin Punch a Abuja, wata majiya ta shaida cewa:
“Za mu gana a yau kuma kwana za a yi domin mu samu isasshen lokacin yanke shawarin karshe.”
Read Also:
Yayin da aka tambaye ta ko kungiyar za ta janye yajin aiki, majiyar ta ki yin bayani a kai, NairaMetrics ta ruwaito.
Matakin yajin aikin ASUU da halin da ake ciki Idan baku manta ba, kungiyar malaman jami’a a Najeriya sun shiga yajin aiki tun watan Fabrairun 2022 a jami’ar Legas.
Gwamnatin Najeriya ta kai ruwa rana da kungiyar, lamarin da har yanzu ba a gama samun mafita mai dorewa ba tukuna.
Kungiyar ASUU ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta cika yarjejeniyar da ta shiga da kungiyar a 2009, ta habaka jin dadin aikin jami’a tare da biyan mambobin ASUU alawus-alawus da take bin gwamnatin.
Ministan kwadago na Najeriya, Chris Ngige ya maka kungiyar ASUU a kotu bayan kai ruwa rana don ganin an warware lamarin yajin.
Kotun ma’aikata ta umarci ASUU ta janye yaji, amma kungiyar ta tubure ta kai maganan gaba, inda nan ma aka sake umartar da ta gaggauta komawa bakin aiki.
Rassan ASUU a jami’o’in gwamnatin sun yi zama makon nan don yanke shawarin komawa bakin aiki.