Kungiyar ASUU ta yi Watsi da Matsayin Farfesa da Aka Bai wa Pantami

Abuja-Ƙungiyar malaman jami’o’i ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.

Punch ta rahoto cewa ƙungiyar bayan taron mambobin majalisar zartarwan ta da ya gudana yau, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, “karan tsaye ga doka.”

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa, Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Litinin.

Shugaban ASUU ya ce:

“Ba zai yuwu ka zama minista kuma kana koyarwa a jami’a lokaci ɗaya ba. Hakan karfafa guiwa ne a saɓa doka.”

“Ya kamata Isa Pantami ya aje mukamin minista ko kuma yunkurin haɗa ayyuka biyu a gwamnatin tarayya. Kwata-kwata bai cancanta ba, dan haka ba za’a ɗauke shi a matsayin Farfesa ba.”

“Mun cimma matsayar hukunta mambobin ASUU da ke da hannu a ƙarin matsayin Pantami da kuma mataimakin shugaban jami’ar FUTO (VC).”

Bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here