Yajin Aiki: Kungiyar ASUU ta Bai wa Gwamnati Wa’adi Zuwa Gobe Talata
Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya wato ASUU ta bayyana cewa a shirye take ta sake shiga wani sabon yajin aiki kan abin da ta kira gazawar gwamnati wajen cika alkauran da aka cimma da ita.
Kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adi zuwa gobe Talata ta tuntube su ko koma ta soma yajin aiki.
Read Also:
Shugaban ASUUn, Farfesa Emmanuel Osodeke a tattaunawarsa da jaridar The PUNCH ta Najeriya ya ce gwamnati ta daina daukan wayarsu.
A watan Maris din 2020, ASUU ta tsunduma yajin aiki bayan rashin jituwa da gwamnati kan kuɗaɗen da take bai wa jami’o’i da wasu tsare-tsaren albashi da alawus-alawus.
An janye yajin aikin ne bayan gwamnatin da ASUU sun sanya hannu kan wata yarjejeniya domin biya musu bukatunsu, yanayin da ya bada damar yanje yakin aikin a ranar 24 ga Disamba 2020.