ASVI: Jahohi 8 ba su da IGR Mai Tsoka

 

Alkaluman Viability Index sun nuna wasu jahohi suna fuskantar barazana.

Wadannan jahohin ba su samun kudin-shiga a shekarar 2020 da ta wuce ba

Irinsu Legas, Ribas, Oyo da Ogun sun tattara abin da ya fi karfin na jahohi 30.

The Economic Confidential ta fitar da rahoton Viability Index watau ASVI da ya bayyana cewa jahohi takwas sun shiga halin ha’ula’i a Najeriya.

Wadannan jahohi suna fama da matsalar kudin-shiga idan aka kamanta da abin da suka samu a 2020.

Alkaluman sun nuna idan aka cire kason da ake ba gwamnonin jahohin daga asusun FAAC, ba su iya tatsar arzikin da zai rike su daga asusun IGR.

Gwamnatocin jahohin suna samun kudin-shiga ne daga tsarin harajin PAYE, harajin hanya da kuma kudi daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Naira tiriliyan 1.3 ne kudin-shigan da jahohin kasar nan 36 suka samu a shekarar 2019 da 2020. Daga ciki jahar Legas kadai ta samu Naira biliyan 418.

Abin da hakan yake nufi shi ne Legas kadai ta samu kudin IGR na jahohi 22 a dunkule. Ta biyu a jerin jahohin da suka fi samun kudi ita ce jahar Ribas.

Yayin da Ribas ta samu Naira biliyan 117 a shekarar bara. Jahohin Kaduna, Ogun sun samu Naira biliyan 50, yayin da Oyo ta iya tara Naira biliyan 38.

Jahar da take ta gaba a jerin IGR ita ce Anambra wanda ta samu Naira biliyan 28 a shekarar bara.

Wadannan jahohi shida da suka fi tattara IGR sun samu Naira biliyan 695. Idan aka tattara ragowar jahohin 30, abin da suka samu Naira biliyan 600 ne.

Jahohi 8 ba su da IGR mai tsoka

Akwai jahohi takwas da ba za su iya rayuwa ba da gudumuwar asusun tarayya ba. IGR dinsu bai kai 10% na abin da suke samu daga asusun FAAC ba.

Jaridar Daily Trust tace wadannan jahohi da suke fuskantar barazana sun hada Bayelsa wanda Naira biliyan 12 ta iya tatsa a kaf shekarar da ta wuce.

Bayan nan kuma sai jahohin Jigawa da Katsina da Naira biliyan 8.6 da Naira biliyan 11.3 kadai ya iya shiga cikin asusunsu, akasin kasonsu na FAAC.

Naira biliyan 8.3 kadai ya shiga asusun gwamnatin Yobe a 2020. Sauran jahohin da ke wannan rukuni su ne Neja, Taraba da Benuwai, duk a Arewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here