Atiku ya yi Martani ga Buhari Akan Kisan Manoma

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa 40 na Maiduguri.

Ya bayyana takaicinsa karara, inda yace gyara tsarin tsaron Najeriya yana daukar dogon lokaci kuma hakan bai kamata ba.

Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda aka kashe, yana mai yi wa mamatan fatan samun rahama.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar , ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno, kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi gaggawar gyara tsarin harkar tsaro a kasar nan.

Atiku ya yi wannan kiran ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, jaridar The Punch ta wallafa.

Dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2019, ya bayyana yadda al’amarin ya bashi tsoro inda yace bai san yadda zai bayyana tashin hankalin da ya shiga ba.

Kamar yadda ya wallafa, “Jikina ya yi sanyi. Ban san kalaman da zan yi amfani da su ba. Ya kamata a ce rayukan ‘yan Najeriya sun fi haka daraja.

“Canza tsarin tsaron kasar nan yana daukan dogon lokaci. Muna musu fatan samun rahama, sannan muna yi wa iyalansu ta’aziyya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here