Atiku Abubakar da Gwamna Obaseki Sun Hada Gwiwa Don Kayar da Jam’iyyar APC a 2023
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce tarurrukan sulhu da ke gudana tsakanin shugabannin PDP na samun sakamako mai kyau.
Abubakar ya bayyana haka a Benin, babban birnin jahar Edo, a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, bayan ganawa da gwamna Obaseki.
A cewarsa, za a karfafa babbar jam’iyyar adawa a kasar don karbe mulki a 2023 daga APC.
Benin, Edo – Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta ya ayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana da kyakkyawan matsayi yanzu don kawar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki daga mulki a 2023.
The News ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan a Benin, babban birnin jahar Edo, inda ya kara da cewa ziyarar wani bangare ne na shawarwari kan yadda za a karfafa PDP don karbe mulki daga hannun APC gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Legit.ng ta tattaro cewa Atiku ya shaidawa manema labarai bayan ganawar cewa tattaunawarsa da gwamna Obaseki ya ta’allaka ne kan mulki, yanayin da kasar ke ciki da kuma yadda za a karfafa jam’iyyar PDP don karbe madafun iko a shekarar 2023.
Ya ce:
Read Also:
“Musamman, mun tattauna game da shugabanci, halin da ake ciki a ƙasar, mun tattauna game da jam’iyyarmu, yadda yakamata a ƙarfafa jam’iyyarmu da kuma karɓar jagoranci a jahohi da dama da kuma gwamnatin tarayya.”
Obaseki yayi kira da a sake gina PDP kafin zaben shugaban kasa na 2023
Gwamna Obaseki ya kuma ce akwai bukatar sake gina babbar jam’iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasa na 2023 domin ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.
Obaseki ya ce:
“Dole ne mu baiwa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa, halin da muke gani a kasashe da dama masu rauni, bayan barkewar cutar ba ta da kyau ko kadan.
“Da farko, muna buƙatar gina wata jam’iyya mai ƙarfi don ceto Najeriya, na kasance a gefe guda, a bayyane yake cewa akwai jam’iyya ɗaya a Najeriya, wanda ita ce PDP.”
Obaseki ya bayyana abin da ya kira karancin abinci mai zuwa da tsadar kayan abinci a matsayin abin tsoro mafi girma a kasar.
Ya kara da cewa a halin yanzu kasar na cikin mawuyacin hali na tattalin arziki a tarihin kasancewarta kasa.
Jaridar The Nation ta kuma rawaito cewa Obaseki ya jinjinawa Atiku saboda gudunmawar da ya bayar wajen cigaban dimokradiyya.
Ya gode wa Atiku kan kyakkyawan jagoranci, shawarwarin da ya ba shi a lokacin zabensa, ya kara da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tattauna ta sirri, kuma ya taimaka masa lokacin da shi da magoya bayansa suka bar APC zuwa PDP.