Atiku Abubakar ya Soki Nade-Naden da Shugaba Tinubu ya yi a Makon Nan
‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya soki nade-naden da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a makon nan.
Fela Durotoye ya shiga cikin masu taimakawa shugaban Najeriya a wajen yada labarai da hulda da al’umma.
Kafin nan an nada Umar Tanko Yakasai, Abiodun Essiet, Abdulhamid Yahaya da kuma Emmanuella Eduozor.
Abuja – Atiku Abubakar mai shari’a da Bola Ahmed Tinubu a kotu a kan zaben 2023, ya sake yin kaca-kaca da mai girma shugaban kasa.
Abin da ya jawo fushin Atiku Abubakar wannan karo shi ne nadin mukaman da Bola Tinubu ya yi, Premium Times ta kawo wannan rahoto.
‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya fitar da jawabi ya ce karin hadimai a fannin yada labarai ba za su ceci Bola Tinubu ba.
Atiku ya ce karya Tinubu ya shirya Mista Phrank Shaibu ya fitar da jawabi na musamman a madadin Atiku Abubakar, ya na zargin shugaban kasar da kafa sashen furofaganda.
Read Also:
Cif Ajuri Ngelale ya tabbatar da cewa shugaban kasa ya nada karin wadanda za su rika taimaka masa a bangaren yada labarai a gwamnati.
Wadanda aka ba aikin sun hada da:
Fela Durotoye, Fredrick Nwabufo da kuma Linda Akhigbe, sai kuma Aliyu Audu da Francis Adah Abah.
Hadimai ba su ceci Tinubu ba Atiku ya ce ko hadimai dubu shugaban kasa Tinubu zai nada, ba za su kubutar da shi daga badakalar da ya tsunduma tsamo-tsamo ba.
“A ranar 18 ga watan Satumba na yi gargadi gwamnatin Tinubu ta fusata saboda ana ta bankado karyarsu, za su kafa sashen furofaganda. Yanzu sun kafa sashen yada labarai da wayar da kan jama’a. wannan ya jawo adadin masu bada shawara kan harkar labarai sun kai 20.
Kusan mutum uku daga cikin wadanda aka nada su na rike da mukami iri daya.
Mun fahimci yadda idon Tinubu ya rufe saboda ya na cikin badakalar karyar takardu kuma FBI za ta tona asirin harkar kwayoyinsa a Amurka.” – Phrank Shaibu
Shaibu ya ce mukarraban shugaban kasa wajen yada labarai sun fi masu bada shawara a kan tattalin arziki yawa saboda furofaganda.