Ba mu da COVID-19 a Jahar Kogi – Yahaya Bello

 

Yahaya Bello ya yi ikirarin babu wanda ya kamu da Coronavirus a Kogi.

Gwamnan ya na da’awar cewa ana yi wa mutane gwajin cutar a jiharsa.

Alkaluman da su ka fito daga NCDC sun nuna mana haka abin yake ba.

Duk da hujjoji baro-baro da ke nuna karancin gwajin COVID-19 tamkar rana a lokacin sallar azahar, gwamnan Kogi ya na ikirarin babu wanda ya kamu.

Bayan haka gwamna Yahaya Bello ya na da’awar cewa jami’ai sun dage da yi wa mutanen jihar Kogi gwaji domin gano masu dauke da kwayar Coronavirus.

Gwamnan ya hakikance a kan cewa cutar COVID-19 ba ta shiga Kogi ba. Premium Times ta ce da aka yi hira da shi a Channels TV, ya kara maimaita wannan.

“A jihar Kogi, mun ce ba mu da COVID-19, kuma hakikanin magana ita ce, ba mu da COVID-19.”

A cewar Bello, jami’an NCDC sun shiga ma’aikatu, kasuwanni, tasha, kan titi, kauyuka da birane su na gwaji, amma duk da haka babu wanda aka samu da cutar.

Bello ya kara da cewa: “Lokacin da aka koma makaranta, an yi wa ‘yan gari da wadanda ba ‘yan gari ba gwaji, kuma ba a samu wanda ya kamu da cutar ba.”

Bayan haka a cewarsa, NCDC ta yi wa duka masu bautar kasa na NYSC, (kusan mutum 700) da ke sansanin Kogi gwajin cutar, ya ce a nan babu wanda ya kamu.

Premium Times ta ce ba gaskiya gwamnan ya fada ba, zuwa ranar 11 ga watan Disamba, alkaluman COVID-19 ya nuna mutane 425 rak aka yi wa gwajin cutar.

Masana su na alakanta karancin masu cutar a Kogi da rashin yi wa mutane da-dama gwaji.

Alhaji Yahaya Bello ya saba sukar yadda ake kokarin yaki da Coronavirus a Najeriya, wanda hakan ya hada shi fada da hukumomi da jami’an lafiya na kasa.

Amma Bello ya ce bayan samun sabani da jami’an lafiya, daga baya ya kyale a rika yi wa mutane gwaji, inda aka yi wata daya ba a samu wani mai COVID-19 ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here