Wani Dan Majalisa Zai Rabawa ‘Yan Yankinsa Zomo

 

Wani dan majalisa Tunji Ajuloopin zai rabawa al’ummar da yake wakilta zomo don samar sana’a da rage taulauci da zaman banza.

Dan majalisar mai wakiltar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-ero a majalisar wakilan tarayya ya kulla yarjejeniya da kungiyar masu kiwon zomo don tallafawa matasa.

Shugaban kungiyar masu kiwon zomon ya bayyana irin muhimmancin zomo da kuma irin ribar da ake samu, har ya kara da cewa matasa zasu rage wa iyaye wahala da dama.

Tunji Ajuloopin, dan majalisa mai wakiltar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-ero a majalisar wakilan tarayya daga Jihar Kwara ya kulla yarjejeniya da kungiyar masu kiwon Zomo, RFA, a wani yunkurin tallafawa marasa aikin yi a al’ummar da yake wakilta.

Mista Ajuloopin yayin da ya ke karbar wakilcin kungiyar a ofishin mazaba ranar Litinin a Omu-Aran ya ce abin zai zama hanyar samar da sana’a ga matasa marasa aikin yi a yankin.

“Ina so nayi wannan don samarwa da al’ummata aikin yi, da yawa daga ciki basu da aikin yi kuma za su gwada wannan, zai taimaka musu kwarai don saukaka rayuwa.

“Zamu kulla yarjejeniya da ku kuma zamu raba wanda zasu ci gajiyar zuwa rukuni rukuni, za ku ba su horo za kuma mu fara da karamin jari,” a cewar sa.

Abdulrahman Femi, shugaban kungiyar RFA ya bayyana cewa dalibai a yankin na iya fara kiwon zomo don su tallafawa iyayen su, ya kara da cewa cikin shekara daya ko biyu zasu iya biyawa kansu.

A cewar sa, daliban yankin na iya dogaro da kiwon zomo don tallafawa iyayensu wajen biyan kudin makaranta, muna da nau’i daban daban wanda a dan kankanin lokaci za su iya kaiwa nauyin kilo 3.5 kuma a siyar a kasuwa.

Mista Femi ya ce fitsarin zomo da kashin sa na da matukar amfani ga manoma, ya kara da cewa za a iya amfani da fitsarin a matsayin maganin kwarin gayayyaki.

Ya ce akwai masu bukatar zomo a kasuwanni a kasar nan, ya kuma ce ana bukatar shi sosai musamman mutanen da basa cin jan nama.

Ya kuma bayyana irin amfanin zomo ga lafiyar bil adama. Kungiyar RFA din ta nada Mista Ajuloopin a matsayin uban kungiya a yankin Omu-Aran, lokacin da suke mika masa zomaye iri daban daban.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here