Ba Siyasa ce a Gabana ba – Muhammadu Sanusi II

 

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa.

Ya ce, ba siyasa ne a gabansa ba, don haka ya ma koma makaranta zai yi PhD a fannin Doka.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su zama masu tausayawa na kasa dasu shine mafita ga Najeriya.

Abuja – Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Muhammmadu Sanusi II ya bayyana cewa baya son zama Shugaban kasa ko shiga harkar siyasa, The Nation ta ruwaito.

Don more lokacinsa, tsohon sarkin ya ce ya sami damar shiga Jami’ar London don karatu a shirin PhD a fannin Doka.

Zai yi rubutu kan “Kayyade dokokin iyali na Musulmi, kayan aikin gyara zamantakewa”.

Da yake jawabi a wajen liyafar karrama shi don murnar cikarsa shekaru 60 a Abuja, Sanusi ii ya ce tsoro da kwadayi sune manyan abubuwa biyu da suka lalata Najeriya.

Ya ce gogewarsa a gidan yari ta sanya shi rashin jin tsoron zuwa gidan yari ko mutuwa.

Sanusi ya jaddada cewa, kasar na da matsala idan har ‘yan Najeriya masu hannu da shuni suka kasa tunanin yadda za su taimaki marasa galihu a kullum.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here