‘Dan Majalisa Mai Wakilatar Akure ta Arewa da Kudu, Omolafe Adedayo ya Mutu

 

Dan majalisa daga jahar Ondo ya riga mu gidan gaskiya bayan karamar jinya da yayi a asibiti.

Hon Omolafe Adedayo Isaac ta kasance dan majalisa mai wakilatar Akure ta Arewa da Kudu Hakazalika ya rike mukamai da dama, hakazalika babban jigo ne a jam’iyyar adawa ta PDP.

Dan majalisar da ke wakiltar Akure ta Arewa da Akure ta Kudu a majalisar wakilai, Hon Omolafe Adedayo Isaac aka “Expensive”, ya rasu. Hon Omolafe ya rasu da misalin karfe 2 na safe a wani asibiti mai zaman kansa a Akure, babban birnin jahar Ondo.

An zabi Omolafe a Majalisar Dokoki ta kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, The Nation ta ruwaito.

An zabe shi shugaban wata karamar hukuma kuma yayi aiki a matsayin Kodineta na shirin SURE-P a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kakakin Jam’iyyar PDP na Ondo, Kennedy Peretei, wanda ya tabbatar da mutuwar, ya bayyana shi a matsayin dan siyasar talaka wanda za a yi kewar sa.

Peretei ya ce mutuwarsa babbar illa ce ga jam’iyyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here