Shugaba Buhari ya Saka Hannu kan Kudirin Dokar Masana’antar Man Fetur

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana’antar ma fetur.

Shugaban ya rattaba hannun ne yayin da yake aiki daga gida saboda zaman killace bayan dawowa daga Landan.

Dokar za ta samar da tsari da gudanarwa mai kyau ga masana’antar man fetur a Najeriya.

Abuja – Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana’antar man fetur.

Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.

Femi Adesina ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana’antar man fetur na shekarar 2021 don zama doka.

“Aiki daga gida cikin keBewa na kwanaki biyar kamar yadda Kwamitin Kula da Shugaban Kasa kan COVID-19 ke bukata bayan dawowarsa daga Landan a ranar Juma’a, 13 ga Agusta, Shugaban ya amince da dokar ranar Litinin, 16 ga Agusta, a cikin kudurinsa na cika aikinsa na tsarin mulki.”

Hakazalika, Femi Adesina ya bayyana cewa, za a yi bikin samar da dokar a ranar Laraba mai zuwa bayan shugaban ya fito daga kebe da yake ciki na kwanaki biyar.

Da yake karin bayani game da dokar, Adesina ya ce:

“Dokar Masana’antar Man Fetur za ta samar da doka, shugabanci, tsari da kasafin kudi ga masana’antar man fetur ta Najeriya, ci gaban al’ummomin da ke zaune a yankunan mai, da abubuwan da suka danganci hakan.

“Majalisar dattijai ta zartar da kudirin a ranar 15 ga Yuli, 2021, yayin da Majalisar Wakilai ta yi haka a ranar 16 ga Yuli, don haka ya kawo karshen dogon jira tun farkon shekarun 2000, kuma hakan karin girma ne ga gwamnatin Buhari.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here