Babu Wanda ya isa ya Hana mu Gudanar da Zaɓen ƙananan Hukumomi a Kano – Gwamna Abba
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce “babu mutuimn da ya isa ya hana mu gudanar da zaɓe a jihar Kano” kasancewar duk jihohi sun yi nasu.
Gwamnan dai ya yi wannan magana ne a cikin gajeren bidiyo da ke nuna gwamnan na yi wa magoya bayansa bayani mai kama da yanayin kamfe.
“Duk jihohin faɗin Najeriya babu jihar da ba ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ba saboda haka ba mu ga dalilin da wasu maƙiya jihar Kano….a yau su fito su nemi su hana mu mu yi zaɓe…….
Read Also:
Jihar Kano a wannan lokacin babu mahaluki da za mu bari ya shigo jihar Kano ya dinga cin mutumcin jihar Kano mu ƙyale shi.” In ji gwamna Abba.
Ya ƙara da cewa “gwamnatin Kano da hukumar zaɓe duka ba mu saɓa kowacce ƙa’ida ba saboda haka muna kan turba kuma za mu yi zaɓe cikin lafiya da lumana.”
A ranar Talata ne dai wata kotun tarayya a Kano a wani hukunci da ta yi ta rushe dukkannin shugabannin hukumar zaɓen jihar Kano mai zaman kanta, KANSIEC bisa abin da ta kira rashin cancanta tare da yin umarnin ka da a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya yi a watan Oktoba, har sai an naɗa mutanen da suka cancanta domin jagorantar hukumar.