Idan ana so Ayi Takara, Bai Kamata ‘Yan Daba su Shiga Cikin Zabe ba – Bashir Ahmad
Bashir Ahmad ya tsaya neman takarar kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya a jihar Kano.
Tsohon Mai taimakawa shugaban Najeriyan ya bada labarin abin da ya wakana a wajen zabe.
Matashin ya nuna an kawo ‘yan daba a wurin da za a fitar da ‘dan takarar Gaya/Ajingi/Albasu.
Kano- Bashir Ahmaad yana neman kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Gaya, Ajingi da Albasu a jam’iyyar APC.
A makon nan ne masu zaben ‘dan takara suke fito da wadanda za su rikewa jam’iyyar APC mai mulki tuta a babban zaben 2023 mai zuwa.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 27 ga watan Mayu 2022, Ahmad ya ce an nemi ayi amfani da ‘yan daba.
Ganin rayuwarsa da na ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da ke shirin kada masa kuri’a a zaben ta na cikin hadari, wannan ya sa dole su ka bar filin zaben.
Hadiman shugaban kasar ya bada labarin abin da ya faru, ya kuma fadawa mutane su saurare shi.
Read Also:
“A matsayin mai neman takara, na bar filin zaben tsaida gwani na zabenmu na Gaya, Ajingi da Albasu a majalisar tarayya
…A dalilin tsaron mafi yawan masu kada mana kuri’a. Idan ana so ayi takara, bai kamata ‘yan daba su shiga cikin zabe ba.
A dakace mu!”
– Bashir Ahmaad
Ahmaad yana sa ran kai labari
Hakan na zuwa ne bayan da kimanin karfe 2:00 na rana, an ji Mai taimakawa shugaban kasar ya na nuna alamun ya hango nasara a tafe.
Bashir Ahmaad ya rubuta: “Nasara, in Sha Allah!” a shafinsa, yana fatan ya lashe zaben gwanin.
A halin yanzu mu na cigaba da sauraron Ahmaad kamar yadda ya ankarar. Matashin yana takara ne da ‘dan majalisan da ke kan kujera.
Siyasar daba a Kano
A kan zargi ‘yan siyasar Kano da amfani da ‘yan daba wajen samun nasara a zabe duk da kokarin da ake yi na tsabtace siyasar Najeriya.
Sha’aban Sharada ya yi irin wannan zargi, ya ce ana neman ganin bayan rayuwarsa a dalilin neman tikitin gwamnan Kano da ya yi a APC.
An ji labari cewa Hon. Sha’aban Sharada mai neman kujerar gwamnan jihar Kano a APC ya na zargin akwai yunkurin magudin da aka shirya.