Atiku Abubakar ya Lashe Zaben Fidda Gwanin ‘Yan Takaran Shugaban Kasa

Bayan sa’o’i sama 15 da deleget suka taru a farfajiyar Velodrome na filin kwallon Abuja, an sanar da sakamako

Alhaji Atiku Abubakar ya samu gagarumar nasara kan Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike

Sauran yan takaran da suka dan tabuka kokarin sune Bukola Saraki, Emmanuel Udom da Bala Mohammed

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party PDP.

Kamar yadda yayi a 2019, Atiku yanzu shine zai wakilci jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Atiku ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri’u 371

Wanda ya zo na biyu shine Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya samu kuri’u 237.

Sannan Bukola Saraki wanda ya samu kuri’u 70.

Shugaban kwamitin zaben, Sanata David Mark, bai sanar da haka a karshe ba har yanzu amma mun tattara wannan sakamako bisa kirgen da akayi kuma aka sanar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here