Muna da Gagarumar Kasa Amma ba mu Godewa Har Sai Mun Ziyarci Kasashen da Muke Makwabtaka da su – Buhari ga ‘Yan Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su dinga godewa Allah duk da halin da suka tsinci kansu a ciki.
Buhari ya sanar da cewa, a kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya fama suke da cin abinci sau daya a rana amma ba hakan bane a Najeriya.
Ya sanar da cewa, a shawagin da yayi a jirgin sama a Kano, ya ga manyan gine-gine da ke nuna cigaba ba kadan ba a fannin kayan more rayuwa.
Kano – Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su gode kan halin da suke ciki a kasar nan idan suka duba yadda wasu kasashe suke.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a dakin taron Banquet na Kano bayan kammala ziyarar da ya kai ta kaddamar da ayyuka a jihar.
Read Also:
Kamar yadda Femi Adesina, hadimin shugaban kasan ya sanar a wata takarda, Buhari ya kwatanta cigaba a ababen more rayuwa a fadin kasar nan matsayin abun alheri.
“Muna da gagarumar kasa amma ba mu godewa har sai Mun ziyarci kasashen da muke makwabtaka da su inda jama’a ke cin abinci sau daya a rana.
“A yayin da nake helikwafta, yawan manyan gine-ginen da na gani da yawan cigaba da na hango a kasa abun farin ciki ne.Mun godewa Allah, Mun godewa Allah, Mun godewa Allah.”
– Shugaban kasan yace.
Channels TV ta rahoto cewa, Buhari yayi kira ga masu kudi da su karfafawa matasa gwiwa inda yace ko Mun so, ko mun ki sai sun bar musu kasar.
“Dole ne su rungumi ilimi saboda amfanin ilimi. Fasaha ta kawo sauki amma babu abinda zai mana ye gurbin koyo. Don Allah ku karfafa gwiwar yaranmu su yi karatu.”
– Yace.
Ya taya Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano murna kan ayyukan da yayi a bangaren more rayuwa inda ya kara da cewa ziyarar da ya kai baya-bayan nan a Kogi, Yobe, Legas da Katsina sun nuna cewa gwamnonin sun yi kokari da iyakar iyawarsu.