‘Yan Majalisar Zartarwa Basu Tattauna a Kan Lamarin Dake Faruwa Game da Ministan Sadarwa ba – Lai Mohammed

 

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Muhammed, yace sam basu tattauna kan lamarin dake faruwa da ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani ba a wajen taron majalisar zartarwa.

Har yanzun dai wasu na cigaba da kira ga ministan ya ajiye aikinsa, wasu kuma na ganin wannan bawani abu bane da zaisa ya aje aikin duba da cewa ya fito yayi bayani.

Lai Muhammed yaƙi yarda ya amsa tambayar da aka masa cewa ko gwamnati zata cigaba da tafiya da ministan ko ba haka ba, kawai yace ba’a kawo zancen a wajen taron ba.

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Muhammed, ya ce yan majalisar zaryarwa basu tattauna a kan lamarin dake faruwa game da ministan sadarwa ba a yayin taron su na ranar Laraba wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A yanzun haka ana cigaba da kira ga ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami, ya sauka daga muƙaminsa ko kuma a sallameshi.

Wasu na cigaba da wannan kira ne saboda wasu kalamai da ministan yayi a baya da suka nuna yana goyon bayan wasu ƙungiyoyin ta’addanci a wancan lokacin.

Sai dai har yazuwa yanzun fadar shugaban ƙasa ta yi gum da bakinta kan lamarin kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan da ake ma wannan zargi dai yana ɗaya daga cikin waɗanda Suka halarci taron majalisar wanda yake gudana ta hanyar amfani da fasahar zamani.

A lokacin da aka tambayi Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, kan zargin yace basu tattauna lamarin ba a wajen taron.

Sai dai yaki yarda ya amsa tamabayar da aka masa cewa ko gwamnatin tarayya ta amince da Pantami ya cigaba da kasancewa a muƙaminsa.

Lai Muhammed ya amsa da cewa: “Ba zance komai dangane da ko gwamnati ta amince dashi ko bata amince ba.

Zan dai iya amsa tambayarku kai tsaye, ba’a tattauna akan lamarin ba a taron majalisar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here