‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan Aikin Gini 3 a Jahar Ondo

 

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan aikin gini a wani yankin jahar Ondo.

Rahotanni daga rundunar ‘yan sanda sun bayyana cewa, an sace mutanen ne ranar Talata.

Tuni hukumar ‘yan sandan ta bada umarnin nemo wadanda aka sacen tare da kame barayin .

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan gini a wani yankin jahar Ondo a ranar Talata da ta gabata.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin wadanda ke aikin gyara yankin Ikaram/kunnu -Akoko na kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jahar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Laraba, sannan ya kara da cewa an sace ma’aikatan ne a ranar Talata.

Ya lura cewa biyu daga cikin ma’aikatan da aka sace sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar, yayin da na ukun ya fito daga jahar Filato.

A cewarsa, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Salami ya ba da umarnin tura ‘yan sanda zuwa yankin don nemowa da kuma kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su tare da cafke wadanda suka ‘yan bindiga.

Kakakin ‘yan sandan ya yi bayanin cewa sauran jami’an tsaro, ‘yan uwa kamar Sojojin Najeriya, da na Hukumar tsaro ta NSCDC da mafarautan cikin gida suma suna cikin aiki.

Ya yi kira ga mazauna yankin da ma jahar baki daya, da su kasance a ko da yaushe tare da kai rahoton duk wani wanda ba su yarda da shi ba da suka lura da shi ga ‘yan sanda a kan lokaci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here