Ni ma Ban Tsallake Sharrin Kungiyar Boko Haram ba – Wani Dan Jarida
Ahmad Salkida, dan jarida kuma dan asalin Jahar Borno, ya dade cikin zargin cewa yana da alaka da kungiyar Boko Haram.
Sai dai, matashin dan jaridar ya sha musanta wannan zargi tare da bayyana cewa shi ma bai tsallake sharrin kungiyar ba.
A wani sako da ya wallafa ranar Laraba, Salkida ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kashe wasu ‘yan uwansa.
Matashin dan jarida, Ahmad Salkida, dan asalin jihar Borno ya koka akan yadda har yanzu wasu mutane da hukumomi ke zarginsa da alaka da kungiyar Boko Haram.
Read Also:
Salkida, mai kamfanin jaridar yanar gizo ta “HumAngle” ya taba yin gudun hijira zuwa ketare sakamakon fuskantar matsin lamba, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.
Dan jaridar na yawan kare kansa tare da ganin baiken masu alakanta shi da kungiyar Boko Haram ko Kuma watsa labaransu.
A wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita domin kare kansa, Salkida ya bayyana cewa shi ma bai tsallake kaidin kungiyar Boko Haram ba.
A cewar Salkida, a yanar gizo ya ga faifan bidiyon kisan gillar da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa wasu ‘yan uwansa na jini.
Kazalika, ya bayyana cewa shi da kansa Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, ya ambaci sunansa tare da yi masa barazana.
Salkida ya nuna takaicin yadda duk da hakan wasu sun gaza fahimta, sun ki yarda cewa bashi da wata nasaba, ta zahiri ko badini, da kungiyar Boko Haram.