Rahin Tsaro: Ba Zan Iya Tafiya Zuwa Jahata Ba – Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa

Wani mamba a kungiyar dattawan Arewa ta ACF ya yanke kauna kan shirin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Kakakin kungiyar, Emmanuel Waye, ya ce ya yanke kauna da gwamnatin Shugaban kasa Buhari wajen kawo karshen matsalar da ya addabi kasar.

Waye ya bayyana cewa ba zai iya tafiya zuwa jaharsa ba, Taraba, saboda tsoro, inda ya kara da cewa hakan yake a tsakanin yan arewa da dama.

Sakataren kungiyar arewa ta kasa, Emmanuel Waye, ya bayyana cewa ya yanke kauna da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake hira a shirin Channels TV na Politics Today a ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, Waye ya yi korafi a kan tabarbarewar rashin tsaro a kasar.

“Ta yaya zan yi imani da mutumin da ke jagorantar irin wannan abun? Na yi imani da shi a lokacin da na bi shi a matsayin mai rahoto sannan ya fatattaki wasu bakin haure da suka zo kashe mu,” in ji shi.

“Lokacin da yake son zama Shugaban kasa, na yi imani da shi. Na shaidi yadda mutumin nan ya fatattaki makiya daga kasarmu a 1983 cike da nasara. Amma a yanzu, an yi garkuwa da mutane 300 a jaharsa.”

Yayinda yake bayyana cewa babu tsaro a arewa gaba daya, Waye ya ce babu dan arewa da ke farin ciki da yawan kashe-kashe da hare-hare da ake kaiwa yankin.

Ta bangaren kakakin na kungiyar Arewa, tsoro ya cika shi a yanzu da yake ganin babu tsaro a hanyar zuwa mahaifarsa a jihar Taraba sakamakon rahoton da ake yawan samu na kashe-kashe da hare-hare.

“Ba zan iya zuwa mahaifata ba a Taraba. Wajen gaba daya yana cikin hargitsi, suna kashe mutane a kullun. Ba a bayyana wannan saboda babu mai a Taraba.

“A arewa gaba daya, akwai rashin tsaro. Ban taba jin ban tsira ba kamar yadda nake ji a yanzu. Me zan ce? Kun ga abunda ke faruwa da mutanenmu,” in ji shi.

Rashin tsaro ya kasance batu da ke tafarfasa a kasar biyo bayan hare-hare da kashe-kashe daga fashi da makami, ta’addanci da sauran abubuwa da ke barazana ga tsaro.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here