Bani da Wata Alaka da ‘Yan Ta’adda – Janar Abdulsalami.A.Abubakar
Tsohon shugaba a Najeriya ya bayyana fushinsa game da alakanta shi da ta’addanci da aka yi a jahar Neja.
Ya bayyana yadda yada jita-jita da karya a kafafen sada zumunta ke jawo kara tabarbarewar tsaro a Najeriya.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su san irin bayanan da suke yadawa da karantawa a kafafen sada zumunta.
Wani tsohon Shugaba a Najeriya, Janar Abdulsalami A. Abubakar (mai ritaya), ya musanta cewa yana da wata alaka da ‘yan bindiga da kuma duk wata kungiyar ‘yan ta’adda a jahar Neja, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma bayyana rahotannin da ke alakanta shi da ayyukansu a matsayin “labaran karya, marasa tushe.”
A cewar wata sanarwa da aka fitar a Minna, Abdulsalami ya yi zargin cewa wasu kafafen yada labarai sun alakanta shi da wani jirgin sama mai saukar ungulu da aka kama yana kai abinci da makamai ga ’yan bindiga a sassan jahar.
Read Also:
Sanarwar na dauke da sa hannun mai taimaka ma janar Abdulsalami kan harkokin yada labarai, Dakta Yakubu Suleiman.
A cikin sanarwar ya nesanta kansa daga irin wannan “mummunan laifin da bai dace da kowane dan kasa mai kishi ba”, yana mai jaddada cewa bisa ka’ida, ya kamata ya yi biris da irin wadannan rahotannin na rashin gaskiya amma dole ne ya kafa hujja.
“Irin wadannan labaran na karya suna jawo kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar kuma bai kamata a lamunta da su ba,” in ji shi.
Ya nuna nadamar yadda mutane za su iya yaudaruwa da irin wannan labarin tare da bata sunan mutane da halayensu, ya kara da cewa: “Ina kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan dabi’un na yaudara kuma su yi taka tsantsan da irin bayanan da suke fitarwa da kuma yada su a kafafen sada zumunta”.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da aiki tukuru tare da yin addu’a don dorewar zaman lafiya a Najeriya, yana mai cewa babu wata al’umma da za ta iya samun daukaka ba tare da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ba.